Rundunar yan sanda Najeriya ta haramtawa ƴan fim amfani da kakinsu a fina-finai

cb578406 14f9 4900 9fe2 c36dcb95a476
cb578406 14f9 4900 9fe2 c36dcb95a476

Sifeta Janar na Yan sandan Najeriya ya gargadi masu shirya fina-finai a kasar da su guji aibanta aikin dan sanda a shirye-shiyensu na talabijin, ba tare da izinin rundunar ba.

IG Usman Baba ya kara da cewa daga yanzu ka da a ƙara ganin wani mutum sanye da kayan ɗan sanda a fina-finai, ba tare da izini ba kamar yadda doka ta tanadar.

Ya ce idan ba haka ba to kuwa duk wanda ya karya doka zai ɗanɗana kudarsa.

Sanarwar da rundunar yan sandan ta fitar ta ce “ka da wani mai shirya fina-finai da ya sake nuna ƴan sanda a matsayin marasa kirki ba tare da izini ba a rubuce daga rundunar yan sanda.”

Sanarwar ta ƙara da cewa ba za ta amince da bayyana aikin ɗan sanda ba a fina-finai, matsawar abin da aka kwaikwaya a aikin ba shi da kyakkyawan tasiri ga al’umma

Masu shirya fina-finai a Najeriya kan kwaikwayi jami’an yan sandan kasar, kuma a mafi yawan lokuta ba a nuna su a mutanen kirki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here