Ma’aikatan hukumar NAFDAC sun janye yajin aikin da suka tsunduma

NAFDAC Abuja 1
NAFDAC Abuja 1

Ma’aikatan hukumar tsaftace sahihancin magunguna da abinci ta kasa (NAFDAC), a yau Litinin sun janye yajin aikin da suka shafe mako shida sunayi a fadin kasa baki daya.

Mataimakin shugaban kungiyar ma’aikatan, Idzi Isua, ne ya tabbatar da janye yajin aikin a yau Litinin.

Mista Isua, ya ce kungiyar ta janye yajin aikin ne biyo bayan yarjejeniyar da suka cimma da hukumar.

Kungiyar dai ta tsunduma yajin aiki tun 21 ga Yuni na shekarar 2021.

Karin bayani yanan tafe

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here