Gwamnatin tarayya ta ayyana Litinin da Talata a matsayin ranakun hutun Sallah karama

Minister of Interior Dr. Olubunmi Tunji Ojo

Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranakun Litinin 31 ga watan Maris da Talata 1 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun karamar Sallah.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida wadda babbar sakatariyar ma’aikatar Magdalene Ajani ta sanya wa hannu.

A cikin sanarwar, ministan harkokin cikin gida na Najeriya Olubunmi Tunji-Ojo ya buƙaci dukkanin Musulmai su rungumi tausayawa da karamci da zaman lafiya, inda ya jaddada muhimmancin nuna soyayya da yafiya da haɗin kai domin gina alumma mai cike da zaman lafiya.

Karin karatu: INEC ta sanar da karbar bukatar yiwa Natasha kiranye a majalisar dattawa

Ya kuma buƙaci alummar Musulmi su yi wa Najeriya addu’ar ɗorewar zaman lafiya da samun ci gaba, kuma ya yi kiran gudanar da bukukuwan sallah lafiya.

Aika, Gwamnatin Najeriya ta ayyana Litinin da Talata ranakun hutun Sallah

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here