Shugaban gwamnatin riko a jihar Rivers Admiral Ibok-Ete Ibas mai ritaya, ya dakatar da duk wasu mukaman siyasa da masu rike da mukamai a jihar nan take.
A wata sanarwa da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin ya fitar a ranar Laraba ya ce an yanke hukuncin ne a karkashin ikon da shugaba Bola Tinubu ya baiwa Ibas.
Wadanda abin ya shafa sun hada da sakataren gwamnatin jiha, shugaban ma’aikata, da dukkan kwamishinoni, shugabannin hukumomi, da ma’aikatu da kwamitoci, da kuma masu ba da shawara na musamman, da mataimaka na musamman, da manyan mataimaka na musamman.
“Wannan dakatarwar ta fara aiki ne daga ranar Laraba, 26 ga Maris, 2025. Jami’an da abin ya shafa za su mika aiki ga manyan sakatarorin ma’aikatalunsu.
Karanta: Gwamnatin tarayya ta ayyana Litinin da Talata a matsayin ranakun hutun Sallah karama
Sanarwar ta kara da cewa, a ma’aikatun da babu Manyan sakatarori, za a mika aiki ga babban darakta ko shugaban gudanarwa.
A ranar Laraba, 19 ga watan Maris ne shugaban kasa, Bola Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin shugaban gwamnatin riko na jihar Rivers bayan da shugaban kasar ya kafa dokar ta baci a jihar.
Shugaban ya kuma dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da dukkan zababbun ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.
Ibas wanda tsohon babban hafsan sojin ruwa ne ya sha alwashin tabbatar da doka da oda a jihar.
Ya kuma yi alkawarin hada hannu da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin an dawo da zaman lafiya a jihar.