An rantsar da shugaban mulkin Jamhuriyar Nijar, Abdourahamane Tchiani a matsayin shugaban kasar na wa’adin mika mulki na tsawon shekaru biyar karkashin wata sabuwar yarjejeniya.
Tiani, Janar kuma tsohon shugaban dakarun tsaron fadar shugaban kasa wanda ya jagoranci juyin mulkin a shekarar 2023, shi ma an kara masa girma zuwa mukamin janar na soja mafi girma na kasar, tare da sanya hannu kan wata doka ta rusa dukkan jam’iyyun siyasa.
An gudanar da bikin ne a ranar Laraba a Niamey, babban birnin Nijar, kuma ya nuna farkon lokacin mika mulki na tsawon shekaru biyar, a cewar Mahamane Roufai, babban sakataren gwamnatin kasar.
Karanta har ila yau: Mai rikon shugabancin jihar Rivers ya dakatar da duk masu rike da mukaman siyasa
Matakin dai ya ci karo da kokarin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS na gayyatar kasar da ta koma cikin kungiyar da kuma maido da mulkin dimokradiyya.
Jim kadan bayan juyin mulkin, Tiani ya ba da shawarar cewa kasar za ta koma mulkin farar hula nan da shekaru uku, amma kungiyar ECOWAS ta yi watsi da shirin tare da yin barazanar yin amfani da karfin soji.
Bayan da aka kasa cimma matsaya, Nijar, tare da Mali da Burkina Faso, sun fice daga kungiyar, matakin da aka yanke a farkon wannan shekarar.