Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da karbar bukatar yiwa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da aka dakatar a majalisar dattijai kiranye.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Sam Olumekun, kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a ya fitar a ranar Laraba a Abuja.
Olumekun ya kuma tabbatar da cewa, a ci gaba da sanarwar da INEC ta fitar a ranar Talata, hukumar ta samu adireshin tuntubar wakilan masu shigar da kara da ke neman a sake kiran Natasha.
Ya bayyana cewa an bayar da lambobin waya da adiresoshin imel na wakilan masu shigar da kara ga INEC a wata wasika da suka aike wa shugaban hukumar, mai kwanan wata 26 ga watan Maris.
Olumekun ya sake tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa tsarin kiran zai kasance a bayyane.
Karin karatu: Wata babbar mota ta murkushe mutum 2 har lahira a Kano- FRSC
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, a ranar Litinin din da ta gabata ne kungiyar masu rijistar zabe daga mazabar Kogi ta tsakiya suka mika takardar koke ga hukumar zabe ta kasa INEC, inda suka bukaci hukumar ta fara shirin dawo da Sanata Akpoti-Uduaghan, sanata mai wakiltar mazabar majalisar dattawa.
‘Yan mazabar a cikin wasikar mai dauke da sa hannun babban mai shigar da kara, Salihu Habib, kuma suka mika wa hedkwatar INEC da ke Abuja ranar Litinin, sun ce daga yanzu ba su da kwarin gwiwa ga Akpoti-Uduaghan a matsayin sanata kuma wakiliyarsu a majalisar dokokin kasar.
A halin da ake ciki, INEC, a ranar Talata, ta tabbatar da karbar takardar, tare da buhunan takardu guda shida da aka ce sa hannun sama da rabin wadanda suka yi rajistar zabe daga mazabar majalisar dattawa su 474,554 ne.
Olumekun a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce adadin na rumfunan zabe 902 da ke yankunan mazaba 57 a kananan hukumomi biyar da suka hada da na Adavi, Ajaokuta, Ogori/Magongo, Okehi da Okene.
Ya kuma tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa hukumar za ta bi tsarinta na shari’a wajen bibiyar koke.NAN