An tuhumi Diezani Alison-Madueke kan zargin cin hanci a kotun Birtaniya

Diezani Alison Madueke
Diezani Alison Madueke

Hukumar yaƙi da manyan laifuka a Birtaniya ta tuhumi tsohuwar ministar man fetur ta Najeriya a kotu, kan laifukan cin hanci.

Ana zargin Diezani Alison-Madueke da karɓar cin hancin miliyoyi barkatai na fam ɗin Ingila daga kwangilolin man fetur da iskar gas, da ta bayar don samun cin hanci.

Wata sanarwa da sashen yaƙi da cin hanci da rashawa na duniya a Hukumar Yaƙi da Manyan Laifuka ta Ƙasa ta ce ana zargin Diezani ta ci gajiyar aƙalla fam 100,000 kuɗi hannu, da samun zungura-zunguran motocin alfarma da ɗaukar jirgin sama na shata don tafiye-tafiye da tafiya hutun alfama da kuma kadarori birjik a London.

Shugaban sashen yaƙi da cin hanci na ƙasashen duniya, Andy Kelly ya ce, “waɗannan tuhume-tuhume, muhimmin abu ne na wani cikakken bincike da sarƙaƙiya a cikin ƙasashen duniya.”

Diezani Alison-Madueke, ‘yar shekara 63, ta kasance a matsayin Shugabar Ƙungiyar ƙasashe Masu Arziƙin Man Fetur (OPEC), kuma ministar man fetur ta Najeriya a tsakanin 2010 zuwa 2015.

Hukumar yaƙi da manyan laifukan ta kuma fitar da bayanai dalla-dalla na ladan kuɗi da ta samu ciki har da kujerun gida da aikin gyaran fuska da ma’aikatan gidaje da ta samu, sannan an yi batun biyan kuɗin makarantar ‘ya’yanta da kyautuka daga kantuna masu sayar da kayan gayu na alfarma irinsu kantin sarƙoƙin yari na Cartier Jewellery da kayan gayu na kantin Louis Vuitton.

Tuni aka rufe kadarori na miliyoyin fam da ke da alaƙa da laifukan da ake zargi a wani ɓangare na binciken da ake ci gaba da yi, a cewar hukumomi.

A bara ne, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya ta ce ta ƙwace kuɗi sama da dala miliyan 153 da kadarori fiye da 80 daga hannun tsohuwar ministar ministar wadda aka yi imani tana zaune a London.

Sai ranar 2 ga watan Oktoba ne, Madueke za ta bayyana a gaban Kotun Majistare ta Westminster.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here