AU ta dakatar da Nijar har sai an dawo da mulkin farar hula

Niger Army
Niger Army

Kungiyar Tarayyar Afirka AU ta sanar da dakatar da Jamhuriyar Nijar daga dukkan harkokinta har sai an mika mulki ga hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum.

A ranar 26 ga watan Yuli ne sojoji suka hambarar da Bazoum kuma suka ci gaba da tsare shi.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya rawaitu cewa, kungiyar ta AU ta sanar da dakatarwar ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, yayin da ta sake nanata kira ga gwamnatin mulkin soja da ta saki Bazoum da komawa barikin.

Kungiyar ta AU ta kuma yi kira ga kasashe mambobinta da sauran kasashen duniya da su guji duk wani mataki da zai iya halasta gwamnatin mulkin soja.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here