Kungiyar SERAP ta shigar da karar Shugaban kasa Bola Tinubu kan “haramtawar da ‘yan jarida da kafafen yada labarai 25 daukar rahoto daga Villa ba bisa ka’ida ba.
Rahotanni sun bayyana cewa, a baya-bayan nan ne gwamnatin tarayya ta janye takardar amincewa wasu ‘yan jarida 25 daga aikin yada labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Sai dai kawai an gaya wa ‘yan jaridar da abin ya shafa a babbar kofar fadar shugaban kasa da su mika tamburan nasu.
A cikin karar mai lamba FHC/L/CS/1766/23 da kungiyar ta shigar a ranar Juma’ar da ta gabata a babban kotun tarayya da ke Legas, SERAP na neman: “umarni da tilasta wa shugaba Tinubu ya janye matakin da aka dauka na dakatar da ‘yan jarida 25 da kuma gidajen yada labarai daga daga daukar rahoto daga fadar shugaban kasa.”