Gwamnatin Kano ta yi Allah wadai da kama tsohon shugaban hukumar karɓar ƙorafi da yaƙi da cin hanci Muhuyi Magaji Rimin Gado da ’yan sanda suka yi

Muhuyi Magaji sabo

Gwamnatin Kano ta nuna damuwa kan kama tsohon shugaban hukumar karɓar ƙorafi da yaƙi da cin hanci ta jihar, Muhuyi Magaji Rimin Gado, da jami’an ’yan sanda suka yi tare da tura shi Abuja.

Wannan na cikin wata sanarwa da kwamishinan shari’a na Kano Abdulkarim Kabiru Maude ya fitar.

Sanarwar ta ce an kama Rimingado ne da misalin ƙarfe biyar da rabi na yamma a ofishin lauyoyinsa da ke kan titin Zariya a Kano, inda aka ce wasu jami’an ’yan sanda dauke da makamai suka kama shi ba tare da nuna wani sammaci ko umarnin kotu ba.

Daga nan aka tafi da shi hedikwatar ’yan sanda da ke Bompai kafin a wuce da shi Abuja da yammacin ranar.

Gwamnatin ta bayyana damuwa cewa wannan lamari na nuna tambayoyi masu alaka da dokokin kasa, musamman sassan da suka shafi ’yancin mutum, damar kare kai a gaban shari’a da kuma neman kariyar hakki.

Haka kuma ta jaddada cewa duk da ikon bincike da bin doka da rundunar ’yan sanda take da shi, wajibi ne a yi amfani da su bisa ka’ida da mutunta martabar dan adam.

Labari mai alaƙa: Amnesty international ta nemi a gaggauta sakin tsohon shugaban hukumar karɓar ƙorafi da yaƙi da cin hanci Muhuyi Magaji Rimin Gado

Gwamnatin ta bayyana yadda aka gudanar da kamen a matsayin abin tayar da hankali la’akari da rashin sanar da hukumomin jihar, musamman a lokacin da ake magana kan lamari mai sarkakiya.

Haka kuma ta ce wannan mataki yana iya haddasa fargaba da ruɗani a cikin al’umma tare da kawo siyasa cikin batu.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa gwamnatin ta bayyana cewa akwai yiwuwar wasu ’yan siyasa daga waje na shirin amfani da hukumomin tarayya don haifar da tashin hankali a Kano da kuma gurgunta yanayin zaman lafiya da kyakkyawan shugabanci da ake ciki a halin yanzu.

Wannan ya biyo bayan binciken da gwamnati ta ce an gudanar wanda ya nuna cewa wannan kame na da nasaba da wasu shari’o’i da ake yi wa wasu mutanen da suka rike muƙaman siyasa a jihar.

Gwamnatin ta ce abin takaici ne ganin yadda aka tura jami’an ’yan sanda fiye da arba’in domin kama shi duk da cewa akwai umarnin babbar kotu da ke hana hukuma ko jami’in tsaro kamawa ko ci gaba da tsangwama a kansa, hakan ya haifar da damuwa kan yadda ake amfani da karfin doka ba bisa ka’ida ba a wani lokaci da ake fama da matsalolin tsaro a kasa baki daya.

Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa jihar na ci gaba da zama cikin kwanciyar hankali tare da bin doka, tana mai jaddada cewa ba za ta lamunci duk wani mataki da ya iya kawo tashin hankali ko cusa siyasa cikin aikin tsaro ba.

Ta bukaci rundunar ’yan sanda ta bayyana a bainar jama’a hujjar wannan kame da tura shi Abuja tare da tabbatar da bin doka da kare hakkin dan kasa.

Ta kuma shawarci jama’a su kasance masu natsuwa da bin doka yayin da ake ci gaba da bibiyar lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here