Gwamnatin Kano ta gargadi ‘yan siyasa da sauran jama’a kan lika takardu da fastoci a wuraren gwamnati

Abba Kabir Yusuf Yusuf 750x430

Gwamnatin Jihar Kano ta gargadi ‘yan siyasa, kamfanoni da sauran jama’a da su daina lika takardu, fastoci da alluna a zagayen hanya da sauran kadarorin gwamnati a cikin birnin Kano, tana mai bayyana hakan a matsayin barazana ga kokarin kawata birni da take yi.

Gargadin na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahir Muhammad Hashim, ya sanya wa hannu, inda ya nuna damuwa kan yadda ake bata kyawun wuraren gwamnati a babban birnin jihar.

Gwamnatin ta ce ta lura da yadda ake kara yawan lika kayan talla a zagayen hanyoyi, tsakar tituna, gefen hanyoyi, gadar sama da sauran wuraren da aka kawata.

A cewar kwamishinan, wannan dabi’a na lalata kyawun ayyukan farfado da muhalli da ake yi, tare da haifar da gurbacewar tsarin gani da kuma lalacewar kayayyakin more rayuwa, baya ga toshe ganin direbobi a muhimman hanyoyi.

Ya bayyana cewa ayyukan kawata birnin ana aiwatar da su ne karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf, a matsayin wani bangare na shirin dorewar muhalli da farfado da martabar birnin.

Ya kara da cewa ana ci gaba da shuka ciyayi da kawata zagayen hanyoyi da hanyoyin kore a cikin birnin, tare da inganta muhalli bisa ka’idojin gine-ginen birane masu jure sauyin yanayi.

Gwamnatin ta sanar da jam’iyyun siyasa, kamfanoni, masu shirya taruka, kungiyoyin addini, hukumomin talla da sauran jama’a cewa an haramta amfani da zagayen hanyoyi da tsakar tituna domin lika fastoci da makamantansu ba tare da izini ba.

Ta bukaci kowa da kowa ya daina wannan aiki nan take, tana mai cewa an umarci jami’an sa ido su kara tsaurara duba domin tabbatar da bin ka’idojin tsaftar muhalli da tsarin tafiyar da birane.

Gwamnatin ta gargadi masu karya doka da cewa za a hukunta su bisa tanadin doka, kuma za su iya daukar nauyin gyara duk wata kadara ta gwamnati da aka lalata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here