Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa EFCC ta kama mutum takwas tare da kwace manyan motoci shida bisa zargin hannu a hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a kan hanyar Ilorin zuwa Ogbomoso da ke jihohin Kwara da Oyo.
Wannan kamen ya kawo adadin mutanen da ofishin hukumar na Ilorin ya kama cikin wata guda zuwa 18 kan zargin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.
A cikin sanarwar da kakakin hukumar, Dele Oyewale, ya fitar a ranar Litinin, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar Asabar bayan samun sahihan bayanan sirri da kuma shafe kwanaki ana sa ido kan hakar ma’adanai da safarar su ba bisa ka’ida ba a wasu sassan jihohin biyu.
Sanarwar ta ce an tare wadanda ake zargin tare da manyan motoci shida dauke da nau’o’in ma’adanai da ake zargin sinadarin lithium da kaolin ne.
Binciken farko ya nuna cewa ana zargin sun gudanar da ayyukan hakar ma’adanai ba tare da lasisi, izini ko amincewar hukumomi ba.
Hukumar ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.













































