Shugaban kasa, Bola Tinubu, a ranar Litinin ya karbi bakuncin gwamnonin jihohi domin buda-bakin watan Ramadan a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, inda ya bukaci hadin kai da shugabanci mai bai wa kowa dama.
Taron ya hada gwamnonin jihohi, mataimakansu da manyan jami’an gwamnati domin buda baki tare.
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, da mambobin majalisar ministoci sun halarci taron.
Da yake jawabi, Tinubu ya gode wa Allah da ya raya su har suka shaida wani watan Ramadan.
Ya ce azumin Ramadan ya zo daidai da lokacin azumin Kiristoci, yana nufin da’a, sadaukarwa, imani, juriya da kaunar juna.
Tinubu ya bukaci gwamnonin su rungumi hadin kai, hakuri da shugabanci da ke bai wa kowa dama.
Ya ce a wannan lokaci na hadin kai da sadaukarwa, ya dace a bai wa matasa dama.
Ya yaba wa gwamnonin kan ci gaban da aka samu a jihohinsu, yana mai cewa ya ga ana samun ci gaba a jihohi.
Tinubu ya ce kasa na kan hanyar shawo kan kalubalen tattalin arziki, yana mai cewa an fita daga yanayin rashin tabbas, kuma abubuwa mafi alheri na tafe.
Ya ce zai ci gaba da karfafa tsaro da bunkasa ci gaba a kasa.
Shugaban ya bukaci shugabanni su kula da marasa galihu tare da yada damammaki ga jama’a.
Da yake magana da manema labarai, gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya ce buda-bakin taro ne na hadin kan addinai.
Ya ce sau daya cikin kimanin shekaru 33 azumin Kiristoci da na Musulmi ke haduwa, kuma hakan na koyar da hadin kai.
Uzodinma ya ce gwamnonin na aiki tare da shugaban kasa domin ci gaban kasa.
Buda-bakin na daga cikin shirye-shiryen da shugaban ke yi a duk watan Ramadan.













































