Zulum ya ziyarci iyalan masuntan da Boko haram ta hallaka

1678558764344
1678558764344

Gwaman jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya Babagana Umara Zulum ya kai ziyara ga iyalan masunta sama da 30 da ‘yan Boko Haram suka kashe a ƙauyen Mukdolo.

A wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa Tuwita, ya ce ya je garin Dikwa inda daga nan ne masintan ke zuwa sana’ar tasu inda mayaƙan Boko Haram suka yi musu kwantan ɓauna, domin jajantawa iyalan mamatan.

Ƙaramar hukumar Dikwa na daga cikin ƙananan hukumomin da Boko Haram ta mamaye a shekarar 2014 kafin sojoji su kore su tare da ƙwace garin.

Gwamnan ya gana da iyalan mamatan a fadar Shehun Dikwa Alhaji Ibrahim Ibn Ibrahim El-Kanemi.

Zulum ya kuma jajanta wa iyalan tare da yin addu’ar neman rahama ga mamatan.

“A madadin gwamnati da mutane, ina miƙa saƙon ta’aziya ga iyalai da ‘yan uwan mamatan waɗanda aka kashe a ƙoƙarinsu na neman na kansu domin ciyar da iyalansu”.

Sanarwar ta ƙara da cewa gwaman ya bayar da tallafi ga iyalan mamatan a lokacin ziyarar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here