‘Yan bindiga sun sace mutum tara a Abuja

BANDITS
BANDITS

‘Yan bindiga sun kai hari tare da sace wasu mutum tara a rukunin gidaje na ‘Grow Homes’ da ke unguwar Kubwa a wajen Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya.

Rahotonni sun ce ‘yan bindigar su kimanin 20 sun yi wa rukunin gidajen dirar mikiya ranar Juma’a da daddare.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan birnin tarayya SP Josephine Adeh ta tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, tana mai cewa bayan da suka samu kiran waya daga yankin, nan take suka tura jami’an ‘yan sanda domin fatattakar ‘yan bindigar.

To sai dai ta ce kafin zuwan jami’an tsaron ‘yan bindigar sun gudu da mutanen da suka sace zuwa cikin daji.

Ta kuma ƙara da cewa ‘yan sanda na ƙoƙari wajen ganin sun kuɓutar da mutanen da aka sacen.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here