An bindige shugabar mata ta jam’iyyar Labour Party a Kaduna

Labour Partys women leader shot dead in Kaduna 715x430 1
Labour Partys women leader shot dead in Kaduna 715x430 1

Rahotanni sun ce an harbe shugabar matan jam’iyyar Labour Party Victoria Chintex a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar shiyyar kudancin Kaduna Edward Buju, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa daya fitar.

Sanarwar ta ce ta rasu ne bayan da wasu ƴan bindiga suka kai farmaki gidanta da ke Kaura suka harbe ta har lahira.

A cewar sanarwar, an kuma ce mijin nata ya samu raunuka a harbin bindiga kuma a halin yanzu yana samun kulawa a wani asibiti.

“Buju, wanda ya bayyana marigayiyar a matsayin mai kwazo da himma da kuma ja-gorancin shugaban jam’iyyar”

Rundunar ƴan sandan Kaduna har izuwa lokacin hada wannan rahoton ba ta ce uffan ba kan wannan lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here