Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da manyan ‘yan kasuwar man fetur a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja ranar Laraba.
Gwamna jihar Ogun kuma shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwar mai, Dapo Abiodun, ne ya jagoranci ‘yan kasuwar zuwa wurin ganawa shugaban ƙasa.
Wannan ganawa ta shugaba Tinubu da yan kasuwan na zuwa ne yayin da ake cece-kuce da yunkurin nuna adawa ta hanya daban-daban da cire tallafin man fetur (PMS) a Najeriya.
Tun a jawabinsa na ranar bikin rantsarwa, 29 ga watan Mayu, a Eagle Square, shugaban ƙasa, Tinubu, ya ƙara tabbatar da cewa FG ta tsame hannunta daga biyan tallafin mai. Shugaba Tinubu ya ce gwamnatin da ta gabata karkashin jagorancin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ba ta ware kuɗin tallafin mai ba a kasafin 2023.













































