Shugaban kasa Tinubu ya shiga ganawa da gwamnonin jihohin Najeriya

IMG 20230605 WA0003 1 750x430 1
IMG 20230605 WA0003 1 750x430 1

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da gwamnonin jihohi Najeriya 36 wadanda suke karkashin kungiyar gwamnonin kasa (NGF) a fadar sa dake Villa Abuja.

Wadanda suka halarci taron sun hada da gwamnan Zamfara, Kano, Taraba, Kogi, Ogun, Nasarawa, Bayelsa, Adamawa, Ebonyi, Lagos, Rivers, Osun, Jigawa, Benue, Taraba, Delta, Enugu, Rivers, Oyo, Plateau, Kebbi, Abia, Imo, da kuma Bauchi.

Sai mataimakan gwamnonin jihar Edo da Niger da suka wakilci gwamnonin su.

Gwamnonin da ba’a fara taron da suba su ne gwamnan Katsina, Kaduna, Gombe, Borno, Cross River, Akwa Ibom, Anambra, Ekiti, Sokoto, da Ondo.

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da kuma sakataren gwamnatin tarayya sanata George Akume na daya daga cikin mahalarta taron.

A ranar Juma’an data gabata dai Tinubu ya gana da gwamnonin jam’iyyar APC.

Karin bayani yanan tafe…..

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here