Wasu ɓata-gari sun farmaki gidan tashar gidan rediyon jihar Kogi da safiyar ranar Talata.
Ɓata-garin sun ƙona gidan rediyan na Kogi Radio 90.5 FM da ke a Ochaja cikin ƙaramar hukuma Dekina, inda suka sace kayayyakin da ke a cikinsa.
Masu gadin tashar gidan rediyon sun sha na jaki a hannun ɓata-garin waɗanda suka ƙona dukkanin wasu muhimman kayayyakin aiki da ke a gidan rediyon.
Wani shaida ya bayyana cewa ɓata-garin sai da suka bi suka sace duk wani muhimmin kayan aiki a tashar gidan rediyon.
A cewarsa har wani janareto ƙirar Mikano da ɗaya daga cikin ƴan takarar gwamnan jihar ya bayar bai tsira ba daga hannun ɓata-garin inda suka yi awon gaba da shi.
A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar ƴada labarai ta jihar, Salawu Patience, ta fitar ta bayyana cewa gwamnatin jihar ta yi Allah wadai da wannan aikin ta’asar, inda ta bayar da tabbacin cewa jami’an tsaro na aiki tuƙuru domin cafke ɓata-garin.
Kakakin ta bayyana cewa kwamishinan ma’aikatar Kingsley Fanwo, tare da darakta-janar na hukumar yada labaran jihar, Alhaji Ojo Oyila Ozovehe, sun kai ziyara gidan rediyon domin ganewa idanunsu irin aika-aikar da aka tafka a wajen.
Shirye-shirye sun tsaya cak a tashar bayan an kulleta saboda ɓarnar da aka yi amma gwamnatin na yin duk mai yiwuwa wajen ganin an ci gaba da aiki a tashar ba tare da ɓata wani dogon lokaci ba.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP William Aya, ya ci tura saboda bai amsa kiran wayarsa ba da saƙon da aka tura masa a waya.













































