Shugaban kasa Bola Tinubu ya rantsar da sanata George Akume a matsayin sabon sakataren gwamnatin tarayya.
An rantsar dashi ne a yau da misalin karfe 11 na rana a fadar shugaban kasa dake Villa Abuja.
Wadan da suka samu damar halartar taron sun hada da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan, gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq da sauran su.