Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad, ya umarci masu rike da masarautin gargagiya na jihar, dasu fara neman izini daga gwamnati kafin su bawa wani mukami a masarautun su.
A baya dai mun kawo muku rahoton cewa gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya tsige sarkin Birnin ‘Yando a karamar hukumar Tsafe, Aliyu Marafa, bisa bawa wani dan ta’adda, Ado Aleru, mukami a masarautar sa da ya yi.
Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar tace ya zama dole masu rike da masarautin gargajiya su bi dokar da gwamnatin ta kafa, don gudun fishin gwamnati.













































