Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), ta kama mutane 105 da suka hada da ‘yan kasar China hudu, a wani rukunin kasuwanci da ke unguwar Gudu a Abuja bisa zargin zamba ta intanet.
Kakakin ta, Dele Oyewale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja
Ya ce an kama su ne a wani samame da jami’an hukumar suka yi.
Oyewale ya ce kama wani bangare ne na kokarin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ke yi na tsaftace al’ummar kasar daga damfarar intanet da sauran ayyukan cin hanci da rashawa.