DA DUMI DUMI: ‘Yan bindiga sun kashe wani babban jami’in Gwamnatin Jihar Kaduna

Gunmen
Gunmen

Wasu ‘yan bindiga su biyar da sanyin safiyar Juma’a sun kashe Daraktan Ayyuka na Hukumar kula da bayanan da shafi kasa ta Kaduna (KADGIS), Malam Dauda.

An tattaro cewa maharan sun yi nasara kan Jami’an tsaron gidan mamacin da ke unguwar Barakallahu a karamar hukumar Igabi ta jihar inda suka kashe shi.

A cewar majiyoyin maharan shi kadai suka kashe sannan suka yi awon gaba da wasu abubuwa masu daraja a gidan.

An kuma tattaro cewa wadanda ake zargin sun kai hari a wata unguwa da ke kusa da su ne domin su karkatar da hankulan al’ummar a yayin da suke gudanar da wannan munanan kisan.

Sai dai ba a samu asarar rai ba a daya harin.

Da yake tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin, babban baturen ‘yan sanda na yankin , Alhaji Muhammad Abdullahi, ya ce jami’an ‘yan sanda na Rigachikun da Barnawa sun ziyarci wurin da lamarin ya faru.

Ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta sasanta tsakanin al’ummar yankin nan da hukumar sojin sama kan wani katon fili mallakin rundunar, wanda al’ummar ke zargin nan ne maboyar bata gari.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ASP Muhammad Jalige, bai amsa kiran da aka yi masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Al’ummar Barakallahu na da tazarar kilomita biyar daga babban garin Kaduna, a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here