Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya ce zai kafa kwamiti domin gudanar da bincike kan gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike.
A baya-bayan nan dai danganta ta yi tsami tsakanin ɓangarorin biyu, har ma gwamna Fubara ya zargi Wike da barwa jihar tarin bashi.
A cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta an ga gwamna Fubara na cewa ”Duk wanda ya ɗauki bindiga da nufin kisa, to in ka samu dama kai ka binne shi.”
Karin labari: Yadda ake shigar da korafe-korafe ga Jami’an ‘Yan Sanda – Jami’i
”Za mu buɗe sabon babi a jihar Rivers, shiru-shiru ba tsoro ba ne, gudun fitina ne, a baya na yi shiru ne saboda mun fito daga gida guda, amma a yadda yake a yanzu, masu iya magana na cewa ɗan zaki ya girma”, in ji Fubara.
Ya ce ”Za mu kafa kwamitin bincike, domin gudanar da bincike kan lamuran gwamnati, kuma ba zan janye wannan mataki ba.”
Karin labari: “Dalilin da yasa na saka Bam a Masallaci” – Wanda ake Tuhuma a Kano
Ya ci gaba da cewa, ”Dole ne mu ci gaba, kuma in dai ci gaba na nufin ɗaukar matakan da ba za su yi wa wasu daɗi ba, to lallai su shirya domin kuwa ba gudu ba ja da baya” in ji gwamnan.
”Watakila wasu na gaya musu cewa ba abin da zai faru ne amma tabbas su sani cewa lallai wani abu zai faru, kuma Allah yana tare da mu, ba za mu bari wani ya yaudare mu ba.”
Da alama gwamnan na jawabi ne a wani taro, domin kuwa a cikin bidiyon ana jiyo muryar wasu na yabawa gwamnan a yayin da yake gabatar da jawabin.