“Dalilin da yasa na saka Bam a Masallaci” – Wanda ake Tuhuma a Kano

Kano, gezawa, 'yansanda, bam, tuhuma, gado
Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano, ta tabbatar da kama wanda ake zargi da kai harin bam a wani masallaci da sanyin safiyar yau a kauyen Gadan da ke...

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano, ta tabbatar da kama wanda ake zargi da kai harin bam a wani masallaci da sanyin safiyar yau a kauyen Gadan da ke karamar hukumar Gezawa ta jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Usaini Gumel, ya shaidawa NAN a wata hira ta wayar tarho a ranar Laraba cewa an kama wani matashi mai shekaru 38 Shafi’u Abubakar kan lamarin.

Karin labari: BUK ta horar da sabbin likitocin lafiya 87 da na hakori 16

Ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin kai hari masallacin ne saboda takaddamar da aka dade ana yi tsakanin dangi kan rabon gado.

“A ranar 15 ga watan Mayu, 2024, da misalin karfe 5:20 na safe ‘yan sanda sun samu rahoton fashewar wani abu a wani masallaci da ke kauyen Gadan a lokacin sallar asuba, wanda ya yi sanadin jikkatar mutane da dama.

Karin labari: Emefiele ya ce bashi da laifi kan buga bayanan kudi na Naira Miliyan 684 da Biliyan 18.96

“Nan da nan, an tura wata tawagar jami’an tsaro, ciki har da kwararru masana abubuwan fashewar sinadarai da Radiyo da kuma Nukiliya (EOD-CBRN), zuwa wurin.

“An garzaya da mutane ashirin da hudu da suka hada da maza 20 da yara hudu wadanda suka samu raunuka daban-daban zuwa Asibitin kwararru na Murtala Mohammed Kano domin yi musu magani,” inji shi.

Karin labari: EFCC ta gurfanar da Emefiele a kotu bisa laifin buga takardun kudi

CP ya ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa fashewar bam ne ya tashi kuma ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike.

Ya ce ‘yan sandan na ci gaba da gudanar da bincike kuma za su fitar da karin bayani nan gaba kadan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here