Alkalin alkalan Nigeria ya nemi a nada wasu alkalan kotun koli guda 6

Ibrahim Tanko Muhammad
Ibrahim Tanko Muhammad

Alkalin Alkalan Najeriya CJN Tanko Mohammad ya bukaci a nada alkalai  a matsayin alkalan kotun koli.

A cikin wata wasika da ta aike wa dukkan jami’an shari’a a Najeriya, CJN ta ce ya zama dole a cike gurbin da aka samu sakamakon kisa da ritaya na alkalai.

“Za ku iya tunawa cewa Hon. Mai shari’a Olabode Rhodes-Vivour ya yi ritaya daga aikin shari’a ne a ranar 23 ga Maris, 2021 bayan ya cika shekaru 70, bisa ga tanadin sashe na 291 na kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya, 1999 (kamar yadda aka yi wa kwaskwarima),” inji wasikar.

“Tun da farko, alkalai Nwali Sylvester Ngwuta da Samuel C. Oseji sun mutu a ranar 7 ga Maris 2021 da 28 ga Satumba 2021, bi da bi.

“Masu shari’a Mary Odili, Ejembi Eko da Abdu Aboki za su yi ritaya daga aikin shari’a a shekarar 2022 bayan sun cika shekaru 70 da haihuwa, kamar yadda dokar kasa ta tanada.

“Saboda haka, ya zama dole a dauki matakin maye gurbinsu a bencin kotun koli ba tare da bata lokaci ba”.

“Zan yi godiya, idan za ku iya zabar ‘yan takarar da suka dace don tantancewa, tare da la’akari da cewa biyu daga cikin kujerun sun kasance na shiyyar kudu maso gabas, daya na shiyyar kudu maso-kudu, daya na kudu maso yamma, daya na shiyyar arewa ta tsakiya da kuma shiyyar siyasa ta arewa maso yammacin kasar.

Kamfanin Dillancin labarai na Nigeria NAN ya ruwaito cewa ana shirin nada alkalai guda 6.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here