Kungiyar Fulani makiyaya Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) ta musanta amincewa da duk wani dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Sakataren na kasa, Alhaji Baba Ngelzarma, ya musanta hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, a Abuja, ranar Laraba.
Sanarwar ta ce kungiyar na mutunta burin dukkan masu neman shugabancin kasar, duk da cewa bai kai lokacin da za a ware wani mutum da zai mara masa baya ba.
Ya ce “an jawo hankalin babbar hedikwatar MACBAN ta kasa kan labaran da ake yadawa a kafafen yada labarai na cewa sun amince da muradin takarar shugabancin kasa na Sanata Bola Ahmed Tinubu.
“Muna so mu bayyana cewa kungiyar ba ta amince da wani dan takara ba.
“Wadanda suka amince da Tinubu suna yin haka ne a matsayin daidaikun mutane, kuma suna da damar yin hakan, amma bai kamata a jawo kungiyar cikin siyasar amincewa da wannan matakin ba,” in ji Ngelzarma.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, a ranar Litinin, 10 ga watan Janairu, ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari kudirinsa na shugaban kasa a 2023.
Tinubu, wanda ya yi magana bayan ganawar sirri da Buhari a fadar gwamnati da ke Abuja, ya ce duk da ya bayyana wa shugaban kasa aniyarsa, zai ci gaba da tuntubar ‘yan Najeriya.
Ya yi watsi da maganar cewa “mai nada sarki ba zai iya zama sarki ba”, yana mai cewa zai so ya karbi mulki daga hannun shugaba Buhari a 2023 don ci gaba da ayyukan alheri na jam’iyyar APC mai mulki.













































