2023: Okorocha ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa

Rochas Okorocha
Rochas Okorocha

Sanata Rochas Okorocha ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress APC.

Tsohon gwamnan na jihar Imo ya bayyana hakan ne a wata wasika da ya aikewa shugaban majalisar dattawa wadda Ahmad Lawan ya karanta a zauren majalisar a ranar Laraba.

Okorocha ya ce zai yi jawabi ga taron manema labarai na duniya a ranar Litinin 31 ga watan Janairu 2022 domin bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a hukumance.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here