An kori jami’an ‘yan sandan dake baiwa mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara, tsaro daga bakin aiki.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na kasa CSP Olumiyuwa Adejobi, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Alhamis.
‘Yan sandan da aka kora dai sune aka gani a wani bidiyo suna harba bindiga sama cikin nishadi lokacin da suke tare da mawakin a garin sa na Kahutu dake jihar Katsina yayin da yaje raba kayan abinci.
‘Yan sandan sun hada da Dahiru Shu’aibu mai mukamin Sufeto da Abdullahi Badamasi mai mukamin Sajan da Isah Dan Ladi shima mai mukamin Sajan.










































