KIDAYA: Ba zamu tambayi abinda ya shafi addini ba – Hukumar kidaya.


Hukumar kidaya ta kasa (NPC) ta yi karin haske kan cewa hukumar kidayar jama’a ta shirya yin tqmbayoyi dasuka jibanci ginshikin addini da kabilanci.

Hukumar ta yi wannan karin haske ne a ranar Juma’a a Kano lokacin da kwamitin yada labarai na kasa kan kidayar jama’a da gidaje na shekarar 2023 ta kai ziyarar ba da shawara ga gidan talabijin na Najeriya, Kano.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa ziyarar ta samu jagorancin Alhaji Lai Mohammed, shugaban kwamitin kuma ministan yada labarai da al’adu, wanda babban daraktan hukumar wayar da kan jama’a ta kasa Dr Garba Abari ya wakilta.

Da yake magana kan rade-radin cewa za a yi wa ‘yan Najeriya tambayoyi kan addinin su da kabilanci, wani mamba a kwamitin, Dokta Isiaka Yahaya, ya ce hukumar ba ta da sha’awar neman irin wadannan bayanai.

Yahaya, wanda shi ne Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar, ya ci gaba da cewa al’amuran addini da kabilanci da ake ta yadawa a kafafen sada zumunta na yanar gizo ne kawai rudani da rashin tushe.

“Tun a shekarar 1991 da Hukumar Kidaya ta kasa ke gudanar da kidayar jama’a, ba mu taba yin tambayoyi kan kabilanci da addini ba.

“Ba mu yi shi a 1991 ba, ba mu yi shi a 2006 ba kuma ba za mu yi ba a yanzu.

” Dalili a bayyane yake. Batutuwan biyu suna da matukar muhimmanci kuma suna da karfin karkatar da hankali daga babban batun kidayar,” inji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here