Zaben cike gurbi: EFCC ta tura jami’an ta 100 Kano da sauran wasu jihohi.

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), ta ce ta tura jami’anta 100 masu makamai domin yaki da sayen kuri’u a Kano, Katsina da kuma Jigawa a yayin zaben da za a yi ranar Asabar a jihohin.

Kwamandan hukumar EFCC na shiyyar Kano, Farouk Dogondaji, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Kano ranar Juma’a.

“Mun tura jami’ai 20 domin sanya ido kan yadda zaben ‘yan majalisar jiha ke gudana a Kafur, Kankara a jihar Katsina,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa an kuma tura isassun ma’aikata domin sanya ido kan zaben a mazabar Tudun Wada/Doguwa, da Takai da kuma wasu zabukan ‘yan majalisar jiha a jihar Kano.

Dogondaji ya ce an kuma tura wasu ma’aikata domin gudanar da zabukan ‘yan majalisar dokoki a Katsina da Jigawa, domin hana sayen kuri’u.

“Mun kuma tura jami’ai zuwa filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano da kuma babban birnin kasar domin sanya ido kan zabukan.

“Zamu fito fili a dukkan runfunan zabe a Kano, Katsina da Jigawa domin sanya ido sosai kan yadda ake gudanar da zabe a lokacin zabe da kuma bayan zabe.

Ya ce an kuma tura tawagar, wani bangare ne na kudirin hukumar na tabbatar da sahihin zabe a yankin.

Dogondaji ya yi kira ga ma’aikatan da su kasance masu kwazo da kwarewa wajen gudanar da ayyukan da aka ba kasa.

Ya shawarci iyaye da kada su bari a yi amfani da ‘ya’yansu ‘yan bangar siyasa, domin duk wanda aka samu da yunkurin tada zaune tsaye za a kama shi a gurfanar da shi a gaban kuliya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here