Hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare, JAMB, ta ce manayan makarantun gaba da sakandre ba su samu damar bawa dalibai damar shiga makarantu ba a shekarar 2021, sakamakon annobar kwarona.
Saboda haka hukumar tace zata zauna da makarantun da kuma masu ruwa da tsaki, ranar Alhamis, don fitar da adadin maikin da dalibai zasu samu, don samun damar shiga manyan makarantun a bana.
Bayanin hakan na dauke cikin wata sanararwa da hukumar ta fitar ranar Litinin a Abuja.
Taron da hukumar zatayi, zai samu halartar shugabanin makarantun gaba da sakandire, shugaban kwamatin ilimi na majalisar tarayya da kuma masu ruwa da tsaki.
Taron zai maida hamkali wajan fitar da adadin makin da dalibai zasu samu don samu damar shiga manyan makarantun kasar nan.












































