Indonesia ta yi barazanar dakatar da kafafen sada zumunta a kasar baki daya

Indonesia to block Facebook Google WhatsApp new
Indonesia to block Facebook Google WhatsApp new

Kasar Indonesia ta yi barazanar dakatar da aikin kafafen sada zumunta na zamani, wanda suka hada da Facebook, WhatsApp da kuma Google a kasar baki daya.

Ministan sadarwa na kasar ne ya sanar da aniyar kasar na dakatar kafafen a yau Talata, idon har suka gaza yin rigista da kasar nan da kwanaki kadan.

Kasar ta basu daganan zuwa Laraba da su kamala yin rigistar samun damar gudanar d ayyukan su a kasar, ko kuma su fuskanci fushin kasar.

Indonusiy ta kafa doka wace ta fara aiki tun a wanatan Junairu na shekarar 2022, wace ta hana duk wani kamfanin sada zumunta na zamani aiki a kasar, batare da yayi rigista da ita ba.

Dokar da gwamnatin kasar kafa na daya daga cikin matakan da gwamnatin kasar ke dauka don rage yada labaran karya, dana tunzura al-umma.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here