Gwamnatin tarayya ta amince da ware kudin Naira Biliyan Shida domin gina manyan makarantu uku a jihar Gombe, a wani mataki da aka dauka domin karfafa bangaren ilimi da kuma inganta ababen more rayuwa a yankin Arewa maso Gabas.
Karamin ministan raya yankuna, Alhaji Uba Maigari Ahmadu, ya bayyana hakan ne a garin Kumo, hedkwatar karamar hukumar Akko, yayin kaddamar da ginin masaukin dalibai mai daukar mutane 250 da hukumar raya yankin Arewa maso Gabas NEDC ta gina.
Ministan ya bayyana cewa hukumar NEDC ce ta gina manyan makarantun uku, a matsayin wani bangare na shirinta na tallafawa jihohin yankin wajen farfado da bangaren ilimi da kuma inganta rayuwar matasa.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa manyan makarantun suna a Dadin Kowa da ke mazabar santoriya ta Gombe ta tsakiya, da Dukku a mazabar santoriya ta Gombe ta Arewa, da kuma Kaltungo a mazabar santoriya ta Gombe ta Kudu.
Ministan ya bayyana cewa wannan yunkuri yana cikin babban shiri na sanya ilimi ya zama abin sha’awa, mai saukin samu kuma mai gasa, musamman a yankunan da suka sha fama da kalubalen ci gaba tsawon shekaru.
Ya jaddada cewa ilimi na da matukar muhimmanci wajen kaiwa matsayin kasa baki daya da kuma rage gibin ilimi tsakanin yankin Arewa maso Gabas da sauran sassan Najeriya, tare da nuni da cewa gwamnatin tarayya na mayar da hankali kan samar da muhallin koyo na zamani da zai karfafa dalibai da inganta sakamakon karatunsu.
NAN ya kuma rawaito cewa manyan makarantun suna dauke da muhimman kayan more rayuwa da suka hada da masaukin dalibai masu inganci, abin da ministan ya bayyana cewa zai taimaka matuka wajen kara mayar da hankali kan karatu da kuma inganta nasarorin ilimi sakamakon yanayi mai dacewa da tallafi.
Ministan ya yabawa gwamnatin jihar Gombe kan hadin gwiwar da ta yi da hukumar NEDC domin tabbatar da cewa ilimi a jihar yana kasancewa mai saukin samu kuma mai jan hankalin duk masu sha’awar karatu, inda ya bayyana hadin gwiwar a matsayin abin koyi wajen samar da ci gaban ilimi mai dorewa da bunkasar yankuna.













































