Rikicin APC ya tsananta a Kano yayin da masu ruwa da tsaki suka gudanar da taruka daban-daban

IMG 20260209 WA0056 750x430

Jam’iyyar APC a karamar hukumar Birni ta shiga wani sabon mataki na rikici bayan bangarori biyu a cikin jam’iyyar sun gudanar da tarukan masu ruwa da tsaki a wurare daban-daban, lamarin da ya kara bayyanar da rabuwar kai da ke tsakanin shugabannin jam’iyyar.

Tarukan, wadanda tun da farko aka shirya su ne domin karfafa hadin kai da dunkulewar jam’iyyar a ciki, sai dai an gudanar da su a wurare mabambanta, abin da ya nuna zurfafa sabani da takaddama tsakanin manyan ‘yan jam’iyyar a yankin.

Daya daga cikin tarukan ya gudana ne karkashin bangaren da ke goyon bayan tsohon gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, inda Shugaban APC na ƙaramar hukumar Birni Alhaji Sani Abubakar Mai Fata Sharada da wasu manyan ‘yan jam’iyyar suka halarta, ciki har da Muntari Ishaq Yakasai, Baffa Babba Dan’agundi, Injiniya Sagir Koki, Salim Hashim Gwangwazo, Nura Hussain, Nabil Sarki Daneji, Ibrahim Kankarofi, Kabiru Labour, Kabiru Rabi’u, Garba Yusuf Abubakar, Aliko Shuaibu Mukhtar da wasu kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman, yayin da Sha’aban Ibrahim Sharada ya aike da uzurinsa.

A daya bangaren kuma, an gudanar da wani taro daban da ke goyon bayan Sanata Barau I. Jibrin a dakin taro na Sultanate Suite, karkashin jagorancin Salisu Maje Ahmad Gwangwazo da Muhammad Ibrahim Kankarofi, inda Salisu Maje Ahmad Gwangwazo, Ibrahim Kankarofi, Hamza Darma, Faruq Iya, Fa’izu Alfindiki, Dan Bello Aminu, Uba Zubairu Yakasai, Injiniya Garba Ahmed Kofar Wambai, Rabi Aminu Me-Mai, Nasiru Hanga, Mu’azzam Marafa, Nasiru Uwe, Dauda Raula da Na Balalu Mai Turare suka halarta, da sauransu.

Rahotanni sun nuna cewa tarukan biyu sun tattauna dabaru tare da yanke wasu shawarwari kan makomar jam’iyyar APC a karamar hukumar, abin da ke nuna yadda kowanne bangare ke kokarin karfafa tasirinsa a cikin jam’iyyar.

Rikicin shugabanci a APC a karamar hukumar Birni ya dade yana gudana tun kafin shigowar Gwamna Abba Kabir Yusuf jam’iyyar, inda ake fama da sabani mai tsawo tsakanin magoya bayan Ganduje da kuma bangaren da ke biyayya ga Sanata Barau.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa a wani lamari makamanci, bangarori masu adawa da juna a cikin APC sun tashi baram-baram a wani taron hadin kai na masu ruwa da tsaki a mazabar tarayya ta Dawakin-Tofa da Tofa da Rimingado, bayan magoya bayan wasu fitattun ‘yan siyasa sun shiga cacar baki mai zafi, lamarin da ya tarwatsa taron da aka shirya domin karfafa dunkulewar jam’iyyar.

Masu nazarin siyasa sun yi gargadin cewa idan har ba a dauki matakan gaggawa na sulhu tsakanin bangarorin kafin babban zaben 2027 ba, ci gaba da wannan rabuwar kai na iya raunana karfin APC a yankin tare da bai wa jam’iyyun adawa damar samun karbuwa a siyasance.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here