Kotun daukaka ƙara tabbatar da dakatar da Natasha

Natasha Akpoti Uduaghan 750x430

Kotun daukaka kara ta sashen Abuja, a ranar Litinin, ta tabbatar da matakin da majalisar dattawa ta dauka na dakatar da Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, daga majalisar.

Kotun ta bayyana cewa majalisar dattawa na da ikon ladabtar da duk wani mambanta da ya karya dokoki, tare da cewa a wannan lamari, ba a tauye hakkin Natasha na asali ba kamar yadda ta yi ikirari.

Yayin yanke hukunci kan karar da Natasha ta shigar domin kalubalantar hukuncin babbar kotun tarayya, Alkalin kotun daukaka kara, Abba Bello Mohammed, ya bayyana cewa bisa tanadin sashe na 66(4) na dokokin tafiyar da ayyukan majalisar dattawa, majalisar na da hurumin daukar matakan ladabtarwa domin tabbatar da tsari da da’a a zaman ta.

Kotun ta ce Sanata Natasha ta yi kuskure a abin da ya faru a ranar 20 ga Fabrairu, 2025, lokacin da shugaban majalisar dattawa ya ware mata sabuwar kujera, amma ta ki amincewa da umarnin.

Kotun ta kuma ce ikirarin Natasha na cewa ba a sanar da ita tun da wuri game da sauya kujerar ba, bashi da tushe, domin babu wani tanadi a dokokin majalisar da ke wajabta yin irin wannan sanarwa tun kafin lokaci.

A cikin hukuncin da dukkan alkalai suka amince da shi, Alkalin Mohammed ya ce babbar kotun tarayya ya kamata tun farko ta ƙi sauraron karar, bayan ta fahimci cewa majalisar dattawa ta yi aiki ne bisa tanadin da ke ba ta damar dakatar da duk wani mamba da ya karya doka.

Kotun daukaka kara ta kara da cewa Sanata Natasha, bayan an sanar da ita sauya mata kujera, ya dace ta koma sabuwar kujerar, tare da jaddada cewa majalisar dattawa ta yi daidai wajen aiwatar da doka ta shida, ka’ida ta biyu, sakamakon ci gaba da kin bin umarnin majalisar.

Kotun ta kuma bayyana cewa kin halartar da Sanata Natasha ta yi gaban kwamitin ladabi, koke-koke da ɗà’a na majalisar dattawa bai taimaka mata a shari’ar ba.

Haka kuma, kotun ta yi watsi da ikirarin Natasha cewa an dakatar da ita ne sabanin umarnin wani alkalin kotu, Obiora Egwuatu, inda ta ce tunda alkalin ya janye kansa daga shari’ar kuma Alkaliya Binta Nyako ta sake fara sauraron ta, umarnin da aka bayar a baya ba ya aiki.

Sai dai kotun ta soki matakin zargin raina kotu da kuma tarar Naira Miliyan Biyar da babbar kotun tarayya ta kakaba wa Sanatar Kogi.

Kotun daukaka kara ta bayyana cewa rashin miƙa takardun doka mai lamba 48 da 49 ga Sanatar Kogi ya zama babban kuskure, wanda hakan ya sa kotun ta soke hukuncin raina kotu da kuma tarar naira miliyan biyar da aka kakaba mata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here