Ma’aikatan aikin ginin hanya Bakwai da aka sace a watan Disambar shekarar 2025 yayin da suke wani aikin hanya na gwamnatin jihar Kwara, sun shaƙi iskar ƴanci bayan shafe makonni da dama a hannun masu garkuwa da mutane.
An sace ma’aikatan ne a ranar 15 ga Disamba a kan hanyar Sabaja zuwa Owa-Onire da ke karamar hukumar Isin, yayin da suke gudanar da ayyukan gina hanya.
Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na ma’aikatar ayyukan gwamnati ta jihar Kwara, Olajide Abolarin, ya fitar a ranar Litinin a Ilorin.
Kwamishinan ayyuka da sufuri na jihar Kwara, Abdulquawy Olododo, ya bayyana cewa ma’aikatan sun samu ‘yancinsu ne ta hanyar hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da hukumomin tsaro.
Ya bayyana sakin nasu a matsayin babbar nasara wajen kare lafiyar al’umma a fadin jihar.
Sanarwar ta yabawa gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, bisa nuna jajircewar siyasa wajen yaki da matsalar rashin tsaro.
Kwamishinan ya kara da cewa daga cikin wadanda aka sako, biyu injiniyoyi ne da ke aiki a ma’aikatar ayyukan gwamnati ta jihar Kwara.
Ya jaddada godiya ga gwamnatin jihar da hukumomin tsaro, tare da nuna jin dadinsa ga duk wadanda suka tsaya tare da su a lokacin wahalar da suka sha.












































