Abdulmumin Jibrin ya bar jam’iyyar NNPP ya koma APC, tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu don yin wa’adi na biyu a 2027

Jibrin 750x430

Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji ta jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC, tare da bayyana cikakken goyon bayansa ga yunƙurin shugaba Bola Ahmad Tinubu na neman wa’adin mulki na biyu a shekara ta 2027.

Jibrin ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya sanya hannu da kansa a ranar Litinin, inda ya ce ya samu kyakkyawan tarba daga dubban magoya bayansa a garinsa na Kofa da ke ƙaramar hukumar Bebeji a jihar Kano.

Ya bayyana cewa al’ummar da suka halarci taron sun amince baki ɗaya da su bar jam’iyyar NNPP da tafiyar Kwankwasiyya domin shiga jam’iyyar APC don marawa shugaba Tinubu baya a yunƙurinsa na yin tazarce.

A cewar Jibrin, sama da malamai 2,000 ne suka gudanar da addu’o’i na musamman domin roƙon Allah ya bai wa shugaba Tinubu nasara, tare da samun zaman lafiya, ci gaba da wadata a Kiru/Bebeji, Kano da Najeriya gaba ɗaya.

Ficewar Jibrin daga jam’iyyar NNPP ta biyo bayan rikice-rikicen cikin gida da suka addabi jam’iyyar musamman a jihar Kano, inda manyan jiga-jigai suka rabu kan shugabanci da tsarin tafiyar jam’iyyar.

Rikicin ya tsananta bayan zaɓen 2023, lokacin da wasu daga cikin manyan ‘yan jam’iyyar, ciki har da Jibrin, suka nuna rashin jituwa da tsarin shugabanci na tafiyar Kwankwasiyya ƙarƙashin jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa tsohon daraktan ƙungiyar tallafa wa Tinubu ne, kuma ya taɓa zama ɗaya daga cikin fitattun ‘yan jam’iyyar APC kafin daga bisani ya koma NNPP a lokacin zaɓen 2023.

Komawarsa cikin jam’iyyar mai mulki ta APC na nuni da wani babban sauyi a siyasar jihar Kano wadda ke ta sauyawa lokaci zuwa lokaci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here