Gwamna Badaru ya umarci jama’a su kai ƙarar duk wanda ya ƙi karbar tsofaffin kuɗi

Mohammad Badaru Jigawa
Mohammad Badaru Jigawa

Gwamnatin Jigawa ta ce har yanzu tsofaffin takardun kuɗin ƙasa na naira 500 da 1000 da Babban Bankin Najeriya ya ce sun daina aiki, kuma Shugaba Buhari ya jaddada hakan, suna aiki a jihar, har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin matasa da wasanni da kuma al’adu, Ibrahim Mamsa, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa a jiya Alhamis.

Gwamnatin Jigawar ta bayyana wannan matsayi ne, da ke zaman bijire wa sanarwar da shugaban ƙasa ya yi, wanda a jawabin jiya Alhamis ya ce naira 200 ce daga cikin takardun uku na 200 da 500 da 1000 za ta ci gaba da aiki, har zuwa ranar 10 ga watan Afirilu na wannan shekara.

Sanarwar ta ce gwamnati ta samu labarin cewa wasu mutane da kamfanoni (bankuna) ba sa karɓar takardun tsofaffin kuɗin a jihar kuma hakan ya dame ta.

Gwamnatin ta buƙaci jama’ar jihar da su kai rahoton duk wani ɗan kasuwa ko wani kamfani ko banki da suka ƙi karɓar tsofaffin takardun kuɗin na naira 200 da 500 da kuma ga hukumar da ta dace a jihar.

Gwamnatin Jigawa na cikin jihohi tara da suka bi sahun gwamnonin jihohin Kaduna da Zamfara da Kogi wajen kai ƙarar gwamnatin tarayya Kotun Koli kan batun canjin kuɗin da Babban Bankin ƙasa ya yi.

Shi ma gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya umarci jama’a a jiharsa su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here