Shugaba Bola Tinubu zai tafi kasar Faransa ranar litinin
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce Tinubu zai koma kasar ne bayan zamansa a kasashen Turai.
“Shugaba Bola Tinubu zai tafi kasar Faransa ranar Litinin, 19 ga watan Agusta, inda zai tashi daga Abuja, babban birnin kasar. Shugaban zai koma kasar ne bayan gajeriyar aikinsa a Faransa,” in ji sanarwar.
Sai dai bai bayyana dalilin ziyarar ba.
Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan da shugaban na Najeriya ya dawo Abuja daga Equatorial Guinea.
Wannan ita ce tafiya ta hudu da Tinubu yake yi zuwa kasar Faransa tun hawansa karagar mulki.
Ya zuwa yanzu, ya je Equatorial Guinea, London, United Kingdom (sau biyu); Bissau, Guinea-Bissau (sau biyu); Nairobi, Kenya; Porto Norvo, Jamhuriyar Benin; Pretoria, Afirka ta Kudu; Accra, Ghana; New Delhi, Indiya; Abu Dhabi da Dubai a Hadaddiyar Daular Larabawa; New York, Amurka; Riyadh, Saudi Arabia (sau biyu); Berlin, Jamus; Addis Ababa, Habasha; Dakar, Senegal da Doha, Qatar.