Badakalar Fili: Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ta tsare shugaban karamar hukuma 

PCCAC PIC B

Hukumar Korafe-korafen Jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano ta kama shugaban karamar hukumar Kiru, Alhaji Abdullahi Mohammed, bisa zargin sayar da fili na sama da Naira miliyan 100 da aka tanada domin yin filin wasa na Kafin Maiyaki.

Mai magana da yawun hukumar Kabir Abba Kabir, ya shaida wa SolaceBase cewa an tsare shugaban karamar hukumar a ranar Juma’a don yi masa tambayoyi.

Karanta: Badakalar Naira Biliyan 20: Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ta damke magatakardar babban kotu, da wasu lauyoyi

Ya ce hukumar ta gano cewa an biya kudaden ne a asusun ajiya na Mohammed, inda wani kamfani mai suna Mahasum ya sayi filayen da aka ware don yin karamin filin wasa da sauransu.

Ya kara da cewa, an tura kudin asusun Mohammed da yawan su ya kai sama da Naira miliyan 240 daga ranar 1 ga watan Nuwambar 2024, lokacin da aka rantsar da shi, zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu, da aka gano shi.

A cewar sa, a halin yanzu Mohammed na bayar da hadin kai wajen gudanar da bincike, da nufin bankado gaskiyar da ke tattare da sayar da fili da kuma gurfanar da wadanda suka aikata laifin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here