NiMet ta yi hasashen kura da hasken rana na kwanaki uku a fadin Najeriya

Sunshine (1)

Hukumar Kula da Yanayi ta ƙasa NiMet, ta yi hasashen kura da hasken rana daga ranar Lahadi zuwa Talata a fadin kasar.

Hasashen yanayi da NiMet ta fitar ranar Asabar a Abuja ya nuna yiwuwar samun ƙurq kaɗan a sassan jihohin Borno, Jigawa, Katsina, Kano, Zamfara da Sokoto a ranar Lahadi.

Sauran sassan Arewa za su kasance da hasken rana a duk tsawon lokacin hasashen.

A yankin Tsakiya kuwa, ana sa ran sararin sama mai haske tare da dan gajimare kadan a duk tsawon lokacin hasashen.

A yankin Kudu, ana sa ran hasken rana tare da gajimare a wasu lokuta.

Daga bisani a ranar Lahadi, ana sa ran yiwuwar tsawa mai dauke da ruwan sama kadan a sassan jihohin Abia, Imo, Anambra, Edo, Ekiti, Oyo, Ondo, Osun, Ogun, Lagos, Delta, Bayelsa, Cross River, Rivers da Akwa Ibom.

A ranar Litinin, ana sa ran matsakaicin ƙura da nisan gani zai kai tsakanin kilomita 2 zuwa 5 a sassan jihohin Kano, Katsina, Bauchi, Gombe, Yobe, Jigawa da Borno.

Sauran sassan Arewa za su kasance da haske tare da kura a sararin sama.

A yankin Tsakiya, ana sa ran hasken rana tare da dan gajimare kadan.

A yankin Kudu, ana sa ran gajimare da hasken rana da safe, yayin da daga bisani ake hasashen tsawa mai ruwan sama matsakaici a sassan Bayelsa, Ogun, Ondo, Edo, Rivers da Cross River.

A ranar Talata, ana sa ran samun ƙura kaɗan a Arewacin kasar a duk tsawon lokacin hasashen.

Yankin Tsakiya zai kasance da hasken rana tare da dan gajimare kadan, yayin da yankin Kudu zai fuskanci gajimare da hasken rana da safe.

Daga bisani, ana sa ran tsawa mai ruwan sama kadan a sassan Ondo, Edo, Bayelsa, Delta da Rivers.

NiMet ta bukaci masu tuki su yi taka-tsantsan idan ana ruwan sama, yayin da ta shawarci kamfanonin jiragen sama su rika samun takamaiman rahoton yanayi daga hukumar domin tsara ayyukansu yadda ya kamata.

Hukumar ta kuma shawarci mazauna yankuna su rika bibiyar sabbin bayanan yanayi daga NiMet, tana mai cewa ƙura na shawagi a sararin sama a Arewacin kasar, don haka jama’a su dauki matakan kariya.

Mutanen da ke fama da cututtukan asma da sauran matsalolin numfashi su kara yin taka-tsantsan kan halin da ake ciki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here