Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ziyarci wurin da gobara ta tashi a kasuwar Singer, inda ya nemi sa hannun Gwamnatin Tarayya wajen samar da kayan aikin kashe gobara na zamani, ciki har da tallafin jirgin sama da sauran muhimman kayan aiki domin taimakawa shawo kan gobarar da kuma hana maimaituwarta a nan gaba.
Gwamna Yusuf ya ce irin wannan sa hannu zai kara karfin hukumomin kashe gobara wajen mayar da martani yadda ya kamata ga lamarin gaggawa a manyan cibiyoyin kasuwanci kamar kasuwar Singer.
Hakan na cikin sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar ranar Lahadi.
Rahoton SolaceBase ya nuna gobarar da ta fara da misalin karfe 4:00 na yammacin Asabar kuma ta ci gaba da tashi har zuwa tsakar dare duk da kokarin hukumar kashe gobara ta jiha, ta tarayya da wasu kamfanoni masu zaman kansu da ke bayar da gudunmawa.
Gobarar kasuwar ta Asabar ta zo kasa da makonni biyu bayan wata gobara ta tashi a kasuwar guda.
Gwamnan ya ziyarci bangaren Gidan Gilas na kasuwar inda gobarar ke ci gaba da tashi da dare, tana lalata shaguna da dukiyoyi.
Yusuf ya yaba da kokarin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano da jami’an tsaro da ke kokarin shawo kan gobarar, ya bukaci ‘yan kasuwa da mazauna yankin su kwantar da hankalinsu tare da bai wa jami’an agajin gaggawa hadin kai yayin da ake ci gaba da kokarin shawo kan lamarin.











































