Cikin Hotuna: Fiye da shaguna 1,500 da kwantena sun kone a gobarar Kasuwar Singer, an yi asara da ta haura Naira Biliyan 5

WhatsApp Image 2026 02 15 at 13.30.39

Shugaban kungiyar ƴan kasuwar Singer, Alhaji Junaid Zakari, ya bayyana sabuwa gobarar da ta tashi a Kasuwar a matsayin mummunar koma baya ga ’yan kasuwa, inda ya bayyana cewa kayayyaki da dukiyoyi da darajarsu ta haura Naira Biliyan 5 biliyan sun lalace a gobarar.

Da yake zantawa ta musamman da jaridar SolaceBase ranar Lahadi, Zakari ya ce fiye da shaguna 1,500, ciki har da kwantena da rumfunan wucin gadi da kananan ’yan kasuwa ke amfani da su, gobarar ta kone su gaba daya.

A cewarsa, bangaren da gobarar ta tashi yana daya daga cikin wuraren da suka fi cunkoso a kasuwar, wanda ke dauke da kayayyaki masu daraja da aka saya da jarin kudi mai yawa.

Zakari ya nuna matukar damuwa kan tasirin tattalin arziki da wannan bala’i zai haifar, inda ya lura cewa ’yan kasuwa da dama suna dogaro gaba daya da ribar kasuwancinsu na yau da kullum wajen ciyar da iyalansu.

WhatsApp Image 2026 02 15 at 13.30.37 768x385

A cewar sa, wannan babban koma baya ne ga mambobinsu, domin wasu ’yan kasuwar suna gudanar da harkokinsu da jarin aro, yayin da wasu ke dogaro da gudummawar kungiyoyin hadaka.

Ya kuma bayyana cewa, an samu nasarar kashe babbar wutar, kuma jami’an kashe gobara suna kokarin kashe sauran ragowar wuta.

WhatsApp Image 2026 02 15 at 13.30.40

Lokacin da SolaceBase ta ziyarci kasuwar da misalin karfe 10:12 na safe ranar Lahadi, hayaki yana ci gaba da tashi daga wasu sassan wuraren da abin ya shafa, ciki har da Gidan Gilas, Gidan Gashash, Gidan Mai, da bangaren Audu Yahaya Danbatta.

An ga jami’an kashe gobara suna kokarin dakile ragowar wutar tare da gudanar da aikin sanyaya wuri domin hana sake tashinta.

Haka kuma an kuma ga wasu ’yan kasuwa suna tona tarkace domin neman abin da za su iya ceto, yayin da wasu ke tsaye a kungiyoyi suna tattauna girman asarar da suka yi.

Alhaji Isa Abubakar, mai shago, ya ce ya yi asarar kayayyaki da darajarsu ta haura Naira Miliyan 200, yana cewa daga Allah muka fito, gare Shi za mu koma.

Abubakar ya yaba wa Yusuf bisa ziyarar da ya kai wurin, wanda ya nuna damuwa da goyon baya ga wadanda abin ya shafa.

Musa Ibrahim, wani dan kasuwa, ya bayyana alhinin sa, yana cewa ya yi asarar kayayyaki da darajarsu ta haura Naira Miliyan 340 a gobarar.

WhatsApp Image 2026 02 15 at 13.30.41

Shi ma wani dan kasuwa, Halifa Abubakar, wanda ke gudanar da harkar (POS) a kasuwar, ya yi korafi cewa ya yi asarar duk kudin da ke shagonsa.

“Na yi asarar duk kudin da ke shagona. Abin da ya fi min zafi shi ne yawancin kudin ba nawa ba ne. Amma asarata karama ce idan aka kwatanta da wadanda suka yi asarar kayayyaki da darajarsu ta kai biliyoyin naira”.

Da aka tambaye shi ya fadi adadin kudin da ya yi asara, Abubakar ya ce ba zai iya tantance adadin nan take ba.

Gobarar, wadda ta tashi da yammacin ranar Asabar, ta ci gaba har zuwa farkon safiyar Lahadi, tana haddasa barna mai yawa da tashin hankali a tsakanin ’yan kasuwa.

Lamarin ya zo makonni kadan bayan wata mummunar gobara a Kasuwar Singer ta haifar da asara mai yawa, wanda ya kara tsananta wahalhalun da masu kasuwanci ke fuskanta a yankin.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a tantance musabbabin gobarar ba, kuma hukumomi ba su kai ga gano abin da ya haddasa tashin ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here