Ana fargabar wasu fasinjojin sun mutu yayin da wani jirgin kasa da ke tafiya ya murkushe tirelar Siminti ta Dangote da keke mai kafa uku, wanda aka fi sani da Adaidaita Sahu.

Lamarin ya faru ne a kan titin Obasanjo a cikin birnin Kano da misalin karfe 11:30 na safiyar Lahadi.
Shedun gani da ido da ke gudanar da sana’o’i a kusa da titin jirgin, sun ce sun ga tirelar ta nufo layin dogo ne a lokacin da jirgin ke gudun.
Shaidu sun ce sun yi yunkurin sanar da tirelar cewa jirgin kasa yana dab da karasowa wajen, amma direban bai lura ba.
“Lokacin da direban tirelar ya yi ƙoƙarin ketare layin dogo, jirgin ya bugi motar da babur din Adaidaita Sahu a lokaci guda,” in ji ɗaya daga cikin shaidun.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Shaidu sun ce an garzaya da fasinjojin da ke cikin babur din asibiti, yayin da direban tirelar ya tsira da ransa.












































