Dan Majalisar Kaduna Ya Rasu Bayan Kwanaki 3 Da Shan Rantsuwa

Madami Garba Madami 720x430 1
Madami Garba Madami 720x430 1

Dan majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Chikun a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Madami Garba Madami ya rasu.

Wata majiyarmu daga yankin ta bayyana cewa ya rasu ne a yau Asabar da safe bayan ya yi fama da jinya.

A ranar 13 ga watan Yuni ne aka rantsar da ’yan Majalisar Dokokin Kaduna wanda marigayin dan jam’iyyar PDP bai samu damar halarta ba saboda rashin lafiya da yake fama da ita.

Daya daga cikin sarakunan gargajiya a yankin mai suna Ibrahim Saleh wanda shi ne Ardon Ardodin Chikun, ya tabbatar wa Aminiya rasuwar dan majalisar.

“Ya rasu yau da safe bayan ya yi fama da rashin lafiya. Ni ma zan ziyarci iyalansa da yamma domin yi masu ta’aziya,” inji shi.

Sannan ya kuma mika ta’aziyarsa ga iyalai da ’yan uwan mamacin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here