Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya yi maraba da gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, cikin jam’iyyar APC, inda ya bayyana cewa ya shiga siyasa ne domin yi wa al’ummarsa hidima.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fice daga jam’iyyar NNPP a ranar Juma’a 23 ga watan Janairu, 2026, sannan ya koma APC a ranar Litinin 26 ga watan Janairu, a wani taro da aka gudanar a fadar gwamnatin Kano, wanda Sanata Barau da sauran manyan jiga-jigan siyasa suka halarta.
Sanata Barau ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Malam Ismail Mudashir, ya fitar, inda ya jaddada aniyarsa ta yin aiki tare da Gwamna Yusuf da sauran masu ruwa da tsaki domin fuskantar manyan ƙalubalen da Jihar Kano ke fuskanta.
Ya tuna cewa shigarsa harkar siyasa sama da shekaru talatin da suka gabata ta samo asali ne daga ƙudurinsa na yi wa mutanen Kano da ƙasar nan baki ɗaya hidima.
Sanata Barau ya ƙara da cewa, da ikon Allah, ya ci gaba da tsayawa daram kan wannan manufa, kuma zai ci gaba da aiki domin haɗin kai, cigaba da bunƙasar Jihar Kano da ƙasa baki ɗaya.
Ya kuma tabbatar da cikakken goyon bayansa ga shugaban ƙasa kuma babban kwamandan rundunar sojin tarayyar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, tare da biyayyarsa ga manufofin shirin sabunta manufa “Renewed Hope Agenda” domin ganin an kai ƙasar matakin da shugabanci zai amfani kowa.













































