Matatar mtai ta Dangote ta ƙara farashin fetur a faɗin ƙasa

Dangote petrol truck

Matatar man fetur ta Dangote ta ƙara farashin man fetur a kowacce lita zuwa Naira 799.

Wannan ƙarin farashi ya biyo bayan ƙarin Naira 100 daga tsohon farashin Naira 699 kan kowace lita da ya fara aiki a ranar 12 ga watan Disamba 2025.

Farashin sayar da man a tashoshin dillancin MRS ya koma Naira 839 kan kowace lita, daga tsohon farashin Nairav 739 kan kowace lita.

Wannan sabon tsarin farashi ya fara aiki ne bayan kammala lokacin bukukuwa a ƙasar.

Matatar ta bayyana cewa da kammala lokacin bukukuwa, an sake daidaita farashin man fetur zuwa matakan da za su iya dorewa domin tallafa wa daidaiton kasuwa na dogon lokaci da kuma sauƙin saye ga jama’a.

Matatar man fetur ta Dangote ta sake tabbatar da ƙudirin ta na tabbatar da daidaiton kasuwa da kuma wadatar man fetur ba tare da yankewa ba a faɗin ƙasar.

Haka kuma ta nuna cewa a lokacin bukukuwan baya-bayan nan, ta aiwatar da wani tsari na wucin gadi na rage nauyin farashi domin rage wa ‘yan Nijeriya matsin kuɗin a lokacin da kashe-kashe ke ƙaruwa.

Wannan shi ne karo na biyu a jere da matatar ke ɗaukar nauyin tsadar farashi a lokacin bukukuwa domin moriyar ƙasa, ciki har da tallafin jigilar kaya a shekarar 2024 da rage farashi a shekarar 2025 domin sauƙaƙa farashi da kwantar da hankalin kasuwa.

Duk da rage farashin, matatar ta zargi tashoshin mai da dama da gaza aiwatar da sabon farashin a lita, lamarin da ya hana ‘yan Nijeriya cin gajiyar rage farashin.

A matsayinta na matatar cikin gida, matatar man fetur ta Dangote na ci gaba da kare kasuwar Nijeriya daga rikice-rikicen shigo da mai daga waje da tangardar samarwa, tare da kasancewa ginshiƙin daidaito a ɓangaren sarrafa man fetur.

Shugaban zartarwa na kamfanin, David Bird, ya bayyana cewa matatar na samar da kusan lita miliyan 50 na man fetur a kasuwar cikin gida a kowace rana, kuma rarrabawa a faɗin ƙasar na tafiya yadda ya kamata.

Ya ƙara da cewa tsarin ƙirar matatar na ba ta damar sarrafa nau’o’in danyen mai daban-daban, wanda ke ba ta damar ci gaba da samar da man fetur ko da a lokutan gyaran kayan aiki, lamarin da ke tabbatar da wadatar mai ba tare da katsewa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here