Hukumar NAHCON ta amince da yin rijistar aikin Hajji a lokacin azumin Ramadan

NAHCON Chairman Prof Abdullahi Saleh Usman sabo 750x430

Hukumar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON ta amince da lokacin azumin watan Ramadan domin baiwa maniyyata damar yin rijistar aikin hajjin shekarar 2025.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban hukumar Farfesa Abdullahi Usman ya fitar ranar Asabar a Abuja, domin murnar zagayowar azumin watan Ramadan na shekarar 2025.

Shugaban ya taya al’ummar musulmi murnar shigowar azumin watan Ramadan, yana mai jaddada cewa “Lokaci ne na zurfafa tunani, da kuma sabonta ibada ga Allah (SWT).

Karin karatu: Ramadan: Kada ku yi amfani da gurbatattun kaya wanen sadaka – Malami ga Musulmai

Usman ya kara jaddada kudurin hukumar na biyan bukatun al’ummar musulmi da kuma tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara.

A cewarsa, Ramadan ba kawai lokacin azumi da addu’o’i ba ne kaɗai, amma dama ce a gare mu na karfafa dankon zumunci, da tausaya wa marasa galihu, da neman yardar Allah a cikin ayyukanmu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here