Hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da Sakandare ta kasa JAMB, ta bayyana ranar Asabar 28 ga watan Yunin bana a matsayin ranar da za ta gudanar da jarrabawar UTME.
A cewar wata sanarwa da mai bai wa hukumar shawara kan harkokin sadarwa, Dakta Fabian Benjamin, ya sanya wa hannu a ranar Lahadi, an shirya jarabawar share fagen ne domin daukar mutane 5,096 wadanda ba a tantance su ba a lokacin rubuta jarrabawar a baya.
Mai magana da yawun hukumar ta JAMB, wanda ya bayyana cewa hakan ya shafi zagayowar UTME na shekarar 2025, ya ce jarabawar mopup din kuma ta wasu mutane 91,742 ce, wadanda ba su halarci jarabawar ba don haka aka sake shirya musu.
A dunkule, an tsara mutane 96,838 da za su rubuta jarrabawar ta mop-up a cibiyoyin gwajin Kwamfuta watau CBT guda 183 a fadin Najeriya.
Hukumar ta ce, ta na ci gaba da magance kura-kuran da ake samu a yayin rubuta jarabawar da kuma rashin iya fasaha a tsakanin cibiyoyin na CBT.













































